Tsakanin Hibernation da Shutdown wanne yafi?

Tambaya: Please don Allah idan zan kashe computer ta, da inyi switch off, ko hibernation wane ya kamata in rinka yi
daga Ishaq Tanimu Jihar Katsina

Amsa
Kashe kwamfuta shi ya fi musamman saboda hibernation yana daukar wani bangare na RAM kuma yana daukar 2gb na space din Computer, kuma yana tara caches na Computer da kuma tara temporary files da ya kamata ita Computer ta yi deleting din su da zarar ta mutu. 
Kashe Computer ta hanyar da ya dace tana sanya komai nata ya koma mazaunin sa da ya dace da shi, yana kashe dukkan wani wuta da ke cikin ta, ya na taimakawa wajen karawa system din kuzari, yana rage mata wahalar tashi, yana kara taimakawa Hardware da Software kara fahimtar juna.

Duk da cewar hibernation yana da amfani musamman lokacin da mutum yake yin aiki da manyan application masu dadewa wurin budewa ko kuma ita kanta Computer tana nauyi wurin tashi. Ko kuma kana yin aikin da ka san idan na sake kunna Computer shi zan cigaba. Ko kuma process na ci gaba da aikin yana daukar tsawon lokaci to ba laifi idan ka sa Computer a hibernation. 
Allah shi ne mafi sani.

Zaku iya samun cikakken bayanai game da Computer ko waya ko intanet a http://www.duniyarcomputer.com 
Duniyar Computer Mujallar hausa wacce aka yi ta domin warware mana matsala akan abin da ya shafi Computer ko Wayar Hannu ko Internet. 
Godiya ta musamman ga masu taimakawa wuri watsa karatun mu a sauran kafafen sadarwa.
37 likes
 • duniyarcomputerTsakanin Hibernation da Shutdown wanne yafi?

 • s_last_bornAssalamu alaikum @duniyarcomputer suna na Salman abubakar yunus daga garin sokoto Ina bukatar kasancewa daya daga cikin daliban wannan makaranta ta Duniyar computer to amma ban sani ba ko kuna da branch a nan garin sokoto? Dan allah idan har akwai a sanar dani inda yake da kuma yadda tsarukan shiga suke. NA GODE
 • imhali@arewa_kutashi
Log in to like or comment.